
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, ya bayyana damuwa kan yadda ake amfani da shafukan sada zumunta wajen yada labaran ƙarya, yana mai cewa sun zama tamkar kungiyoyin ta’addanci.
Ya yi wannan jawabi ne a taron kwamitin zartarwa na majalisar sarakunan Arewa karo na bakwai da aka gudanar a Maiduguri jihar Borno.
Sarkin ya ce bai kamata a bar al’umma su dogara da labaran da ke yawo a shafukan yanar gizo ba, domin hakan na ƙara tabarbarewar tsaro a ƙasar.
Sarkin ya kuma nuna damuwa kan hare-haren da ake kaiwa a Filato da wasu yankuna, yana mai cewa lamarin na buƙatar kulawa cikin gaggawa.
Rahotanni sun nuna cewa mutane 54 ne suka mutu a wani hari da aka kai a Filato, inda daruruwan mutane suka rasa matsugunansu.
Kungiyar Amnesty International ta ce mazauna yankin na cikin fargabar yiwuwar sake kai hari.