
Kungiyar masu sana’ar hakar zinare a jihar Zamfara sun koka da yadda wasu ‘yan sanda da aika ce nan bogi ne ke tare mutanen da kwace musu kudi da sauran kayan amfani.
Kakakin kungiyar Aliyu Adamu Almajir Gusau ne yayi koken a hirarsa da manema labarai a ranar Lahadi.
Wadanan mutane dake sojan gona sun addabe su, a don haka muke neman daukin gwamanati domin maganin matsalar” in ji shi.Shugaban kungiyar Ya kuma ce, tuni bincike ya wanke ‘ya’yan kungiyar daga zargin hannu cikin ayyukan ta’addanmci da ake yi a jihar Zamfara.
Wanda hakan ya tabbatar da abin da suka dade suna fada cewa aikin hakar zinare ba shi da wata alaka da ayyukan ta’addanci da yankin ke fama da shi.
Kakakin kungiyar Aliyu Adamu, kakakin kungiyar ya ce, babbar matsalar da suka fuskanta a yanzu shine yadda masu saye basa iya shiga inda sule yin sana’ar, domin sayen zinaren da suka hako. Sai, ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wajen tabbatar da doka da oda a wurin.