Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai sanya hannu a yau Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, kan dokokin gyaran haraji guda huɗu da suka samu amincewar majalisun dokoki na tarayya, a wani mataki da ake ganin zai sauya tsarin haraji da tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce bikin sanya hannun zai gudana a fadar shugaban ƙasa tare da halartar manyan jami’an gwamnati.
Cikin waɗanda ake sa ran za su halarta akwai shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, shugabannin kwamitocin kudi na majalisu, shugaban kungiyar gwamnoni, ministan kudi da kuma babban lauya na ƙasa.
Dokokin da za a sanya hannu a kansu sun haɗa da Kudurin Dokar Haraji na Najeriya, Kudurin Dokar Gudanar da Haraji, Kudurin Kafa Hukumar Tara Haraji ta Najeriya, da Kudurin Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Tara Haraji.
