Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga birnin tarayyar Abuja a yau Asabar, domin kai ziyarar aiki zuwa jihohin Borno da Bauchi da kuma Lagos.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai fara ziyararsa ne a jihar Borno, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Babagana Umaru Zulum da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya suka aiwatar.
Yayin ziyarar a Maiduguri, Shugaban ƙasar zai kuma halarci daurin auren Sadeeq Sheriff, ɗan tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff.
- Tinubu Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2026
- Shugaba Tinubu Ya Nada Dambazau a Matsayin Jakadan Najeriya
- Tinubu Ya Sake Nada Buba Marwa A Matsayin Shugaban NDLEA
Daga nan, Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai wuce jihar Bauchi domin yin ta’aziyya ga gwamnatin jihar da kuma iyalan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda Allah yayi masa rasu a ranar 27 ga Nuwamba.
Bayan ziyarar ta’aziyyar, Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai tafi jihar Lagos, inda ake sa ran zai yi hutun ƙarshen shekara.
