Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da shirin kafa kamfanin bayar da bashi na gwamnati da nufin saukaka bayar da bashin ga yan Najeriya.
A sakonsa na murnar shiga sabuwar shekarar 2025, Tinubu ya ce za su yi hadin gwiwa da bankin masana’antu da wasu hukumomin kudi har ma da ma’aikatun gwamnati wajen kafa kamfanin.
Ya kara da cewa, wannan shirin zai kara inganta bangaren hada-hadar kudi da kara fadada hanyoyin samun bashi da kuma bayar da goyon baya ga bangarorin da ba a cika damuwa da su ba, kamar mata da matasa.
Tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a 2023, shugaba Tinubu ya yi alkawarin sake fasalin karbar bashi domin habaka tattalin arzikin Najeriya.