
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a sake nazarin tsarin karɓar haraji a manyan hukumomin da ke samar da kuɗaɗen shiga a Najeriya.
Hukumomin da wannan umarni ya shafa sun hada da, Hukumar Tattara Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS), Hukumar Hana Fasa-Kwauri, Hukumar Kula da Man Fetur ta NUPRC, Hukumar Kula da Jiragen Ruwa (NIMASA), da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC).
An bayar da wannan umarni ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar a ranar Laraba, inda Shugaban Kasa ya jaddada cewa manufarsa ita ce inganta tsarin karɓar haraji daga masu biyan haraji, rage asarar kudaden shiga, da kuma ƙarfafa walwala ta hanyar buɗe sabbin hanyoyin ci gaban tattalin arziki.