Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya sake bai wa shugaban jam‘iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Ganduje da Dr Naisru Yusuf Gawuna da wasu mutane 40 mukamai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Kasa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce tsohon gwamnan na Kano an bashi mukamin shugaban Hukumar Gudanarwa na Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Sama Ta Kasa FAAN.
Dakta. Nasiru Yusuf Gawuna kuma an ba shi mukamin shugaban hukumar gudanarwar Bankin bayar da lamuni na Kasa.
Sanarwar ta ce, wadannan sabbin mukamai ba za su yi katsalandan ga ayyukan shugabannnin hukumomin da gwamnati ta sanar tun da farko ba