
Sugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar cibiyar Al’adu da fasaha ta Wole Soyinka, wadda aka fi sani da National Theater dake Iganmu a birnin Lagos
Taron ya samu halartar shugaban da mai dakinsa Remi Tinubu,
sai mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da Farfesa wole Soyinka, da Gwamnan Lagos Baba Jide Sanwo olu da sauran manyan baki
Gwamnatin tarayya ce dai ta bada kwangilar sake sabunta cibiyar bayan hawan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a 2023 domin farfado da nune nunen al’adu da fasahar zane zane.