
Shugaba Tinubu tare da Kwankwaso a fadar shugaban kasa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin guda daga cikin abokansa masu ra’ayin kawo sauyi a siyasa.
Tinuubu ya yi hakan ne a cikin wani sakon taya murna ranar haihuwar kwankwaso shekara 69 a ranar Litinin.
Sanarwa da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Yada Labarai Bayo Onanuga ya sa hannu.
“Shugaba Tinubu ya taya dangi, abokai da ‘yan siyasar Kwankwasiyya murnar wannan rana ta musamman.
“Ko da yake Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki, amma har yanzu yana rike da manufofin ci gaba.” In ji Tinubu a cikin sanarwar.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba da gagarumar gudummawar da Kwankwaso ya bayar wa ƙasa a matsayinsa na jagora a wurare daban-daban.
“Kasancewar sa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a jamhuriya ta uku da aka soke, Gwamnan Jihar Kano har sau biyu, Ministan Tsaro, da kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Kwankwaso ya bar tarihi kuma ya taka muhimmiyar rawa a ci gaban ƙasa.
“ƙara karɓuwar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Arewacin Najeriya, musamman a Jihar Kano, na nuna irin siyasar jin ƙai da goyon bayan talakawa da yake yi, wadda ke tunatar da siyasar marigayi Malam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
Shugaba Tinubu ya kuma ce sanayyarsa da Kwankwaso ba ta yanzu bace.
“Sanata Kwankwaso abokinsa ne kuma abokin tafiya tun lokacin da suka yi aiki tare a Majalisar Tarayya a 1992, sannan kuma a matsayin gwamnonin jihohi a 1999.
Mun haɗa kai wajen kafa jam’iyyar APC duk da cewa daga baya Kwankwaso ya bar jam’iyyar ya kuma kafa NNPP”. In ji shugaba Tunubu
A karshe Shugaba Tinubu ya yi masa fatan lafiya da kuma ƙarin shekaru masu albarka domi ci gaba da bada gudummawa ga cigaban ƙasa.