
Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Arewa ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara.
Shugaban Ƙungiyar Alhaji Abdullahi Yelwa ne ya yi kiran, yana mai bayyana irin hasarar da rusau din ya janyo wa ‘yan arewa hasarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
“Rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, hakan bai bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci”. In ji shi.
Kungiyar ta kuma roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya su sa baki a maganar don tabbatar da kare haƙƙin ’yan Arewa da suke zaune a Legas.
Haka kuma ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sake duba matakin, ya samar da diyya da shirin sake mazauna kasuwar.
Sai dai Gwamnatin Jihar Legas ta kare kanta, tana mai cewa rushe kasuwar na daga cikin aikin da ta ke yi gyaran birnin domin ƙara inganta tsaro da kuma tsarin kasuwanni.
Masana tattalin arziki na gargaɗin cewa ruguza kasuwar zai iya shafar harkokin kasuwanci da kawo hauhawar farashi da rage harajin da jihar take samu daga irin waɗannan kasuwanni.