
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci majalisar zartarwa ta tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakai masu tasiri domin sauƙaƙa farashin abinci a faɗin Najeriya.
Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron horarwa ga manema labaran majalisar dattijai da aka gudanar a birnin tarayya Abuja a jiya.
Sanata Sabi ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya bayar da umarni ne musamman kan bukatar tabbatar da sauƙin jigilar amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni, domin rage tsadar sufuri da ke ƙara wa abinci farashi.
Ministan ya kuma ce shugaban ƙasa yana da burin ganin an samar da tsarin da zai tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na samun, abinci mai araha, abinci mai inganci kuma mai gina jiki, ba kawai abinci mai yawa ba.
Ministan ya ce gwamnati za ta kaddamar da shirin Farmer Soil Health Scheme don inganta amfanin gona da kuma sabunta tsarin haɗin kan manoma domin samar da kudade da karfafa gwiwar manoma a karkara.