
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin watanni 12.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Sunday Dare, ya bayyana a ranar Litinin cewa shugaban ya amince da daukar wannan mataki don hanzarta kammala aikin.
A watan Janairu, gwamnatin Tinubu ta sanar da sauya kwangilar aikin ga wani sabon kamfani bayan kwace ta daga hannun Julius Berger.
Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na inganta zirga-zirga da kasuwanci a yankin.
