Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura jakadu huɗu daga cikin jakadu 68 da Majalisar Dattawa ta tabbatar da su a watan Disambar da ya gabata.
Daga cikin waɗanda aka amince da tura su akwai Ambasada Ayodele Oke, wanda aka naɗa a matsayin jakadan Nijeriya zuwa Faransa, da kuma Kanal Lateef Are (mai ritaya) a matsayin jakadan Nijeriya zuwa Amurka.
Haka kuma, Shugaban Ƙasa ya amince da tura Ambasada Amin Dalhatu, tsohon jakadan Nijeriya a Koriya ta Kudu, a matsayin Babban Kwamishina (High Commissioner) zuwa Birtaniya.
A gefe guda, Usman Isa Dakingari Suleiman, tsohon gwamnan Jihar Kebbi, an naɗa shi a matsayin jakadan Nijeriya zuwa Turkiyya, ƙasar da Shugaba Tinubu ke shirin kai ziyara ta ƙasa a mako mai zuwa.
A wata takarda da ya aikawa Ma’aikatar Harkokin Waje, Shugaban Ƙasa Tinubu ya umarci ma’aikatar da ta sanar da gwamnatocin ƙasashen huɗu game da nadin jakadun, bisa ƙa’idojin diflomasiyya da aka tanada.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa tura jakadun na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da dangantakar Nijeriya da ƙasashen duniya.
