
Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara a fadin Najeriya, a wani mataki na fadada damar samun ilimi ga ‘yan kasa.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana wannan ci gaba ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Abuja, bayan taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Alausa ya bayyana cewa jami’o’in da aka amince da su sun hada da;Jami’ar Tazkiyah dake jihar Kaduna, Jami’ar Leadership dake babbar Birnin tarayya Abuja, Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara, Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo, Jami’ar Greenland dake jihar Jigawa, Jami’ar JEFAP a jihar Neja, Jami’ar Azione Verde dake jihar Imo, Jami’ar Unique Open a jihar Legas, sai Jami’ar American Open dake jihar Ogun.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta karbi buƙatu 551 na kafa sabbin jami’o’i daga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu, kafin ta aiwatar da tsauraran matakan tantancewa kafin amincewa.