Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ce, rashin amincewa da shi a matsayin minista ba laifin Majalisar Dattawa ba ne, shugaba Bola Tinubu ne bai so ya ba shi mukamin ba.
“Duk da majalisar ta gaza tantance ni a watan Yuli 2024 bisa dalilan tsaro, hakikanin dalili shi ne Tinubu bai saka ni a cikin tsarin gwamnatinsa ba”. In ji shi a hirarsa da Arise News.
Duk da haka tsohon gwamnan ya ce, ba zai taba komawa PDP ba, domin a cewarsa, jam’iyyar adawar ta kara lalacewa.
Ya kuma soki jam’iyyarsa ta APC, yana mai cewa ta kauce daga manufofinta na asali.
Yana mai ikirarin cewa, duk ko da yake ya ja baya daga jam’iyyar APC, ba zai fice daga harkokin siyasa gaba daya ba.
