
Daga Kamal Umar Kurna
Gwamnatin jihar kano ta buƙaci shugaba Tinubu da ya ɗauke sarkin kano na 15 daga jihar kano.
La’akari da yadda wasu ke amfani da damar wajen neman tayar da husuma a jihar.
Mataimakin gwamnan kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan,
“Zaunar da sarkin na 15 a gidan Nasarawa anyi shi ne da niyyar hana gwamnatin kano zama lafiya da kuma ƙin yiwa al’ummar jihar nan abin da ya dace.”
zanga-zangar da wasu daga cikin al’ummar Kano suka fito a ranar Laraba wata alama ce ta neman ‘yancin su kan abin da suke so, na buƙatar a cire sarkin kano na 15 daga gidan na Nasarawa amma aka turo jami’an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga ciki”. In ji shi.
Gwarzo ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa da ya gaggauta ɗauke sarkin daga cikin jihar Kano gaba daya domin barin al’umma su zauna lafiya.
Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa yadda doka ta kawo tsohon sarkin haka doka ce ta kawo sabon sarkin dan haka abar doka ta yi aikin ta.