Gwamnatin tarayya ta karyata labarin cewa Shugaban Tinubu zai je Amurka don ganawa da mataimakin shugaban Amurka, J.D. Vance kan ikirarin shugaba Trump na kawo hari Najeriya.
A cewar Temitope Ajayi, Babban Mataimakiya Ta Musamman Ga Shugaba Tinubu Kan Harkokin Yada Labarai Da Wayar Da Kai da ta fitar a ranar Lahadi.
“Duk wani rahoto da ke ikirarin cewa Tinubu zai tafi Amurka ranar Talata, 4 ga Nuwamba, 2025, don ganawa da mataimakin shugaban kasar, karya ne
“Idan Tinubu zai ziyarci fadar White House, shugaban Donald Trump zai gana da shi, ba mataimakinsa ba.” In ji Ajayi.
Hasashen ganawar ya samo asali ne daga tashe-tashen hankula na baya-bayan nan biyo bayan kalaman shugaban Amurka Donald Trumpna na shirin kai harin soji kasar a bisa zargin kisan gilla kan Kiristocin kasar.
Zargin da gwamnatin ta musanta tare da cewa, siffanta Najeriya a matsayin mai tsattsauran ra’ayin addini bai nuna ainihin halin da ake ciki a kasar ba.
