
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026
Ragi kuma na nan take, sannan hukumar kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban yayin wani taro da ya yi da shugabanni da kuma mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, a ranar Litinin.
Aminiya ta rawaito Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar.
kuma bukaci masu ruwa da tsaki su gaggauta biyan kuɗaɗen da suka dace zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN) domin tabbatar da cika tsare-tsare da kuma gudanar da aikin Hajjin cikin lumana.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da karin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara na miliyan Takwas.