
Gwamnatin Rwanda ta ce ta amince ta karɓi baƙin haure kusan 250 daga Amurka.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, za a ba baƙin hauren horo na aiki da kiwon lafiya da kuma tallafin masauki yayin da suka isa ƙasar.
An bayar da rahoton cewa tuni Amurka ta aika da sunayen farko na mutum 10 domin tantancewa.
Gwamnatin Trump na ci gaba da tsaurara aniyarta na korar miliyoyin baƙin haure da suka shiga Amurka ba bisa ka’ida ba.