Rundunar ‘yan sandan a jihar Benuwe ta sanar da kama wasu mutane 14 a bisa zargin hannu a zanga-zangar da aka yi a Makurdi, babban birnin Jihar, a ranar Lahadi .
A cewar rundunar, zanga-zangar ta fara ne ta shataletalen Wurukum a matsayin martani kan tabarbarewar tsaro a jihar, amma daga baya ta rikide zuwa tarzoma bayan wasu bata-gari sun shiga suka nemi tayar da hankali.
Rundunar ta ce lamarin ya dagule ne lokacin da masu zanga-zangar suka ki sauraron jawabin Mataimakin Gwamnan jihar, Barista John Ode, da Kwamishinan ‘Yansanda, CP Ifeanyi Emenari wadanda suka ziyarci wurin don kwantar da hankali.
DSP Udeme Edet, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ya bayyana cewa, jami’an tsaro sun yi amfani da dabarun kwantar da tarzoma masu sauki, ciki har da harba hayaƙi mai sa hawaye da kuma fesa ruwan zafi, don tarwatsa masu tayar da hankalin da kuma kare lafiyar Mataimakin Gwamnan.
