Daga Nafiu Usman Rabiu
An haifi Sheikh Dahiru Bauchi ne a Gombe, a ranar Laraba 29 ga watan Yunin 1927 miladiyya.
Wanda ya yi daidai da 2 ga watan Al Muharram shekarar 1346 Hijiriyya.
Mahifinsa mutumin jihar Bauchi ne, yayin da mahaifiyarsa kuma ‘yar jihar Gombe ce, kuma dukkanninsu Fulani ne.
Yana kuma da ‘ya’ya sama da 80, wadanda a cikinsu wadanda suka haddace Alkur’ani sun kai 73 ko 74.
Malamin ya rayu a gaban mahaifinsa kuma ya haddace Alkur’ani a wurinsa, kafin ya tura shi nema da kuma ya gyara tare da karo karatunsa a garuwa daban daban.
“Na samu nasarar kara fahimtar haddar Alkura’ani mai girma a wuraren da na tafi neman karatun.
Har sai da ta kai mahaddata na wancan lokaci na kiranna da Goni ko kuma Gangarau, saboda karfin hadda ta Alkur’ani mai girma da yake da ita”. In ji marigayin a hirarsa da BBC.
Shwhun Malamin ya kuma ce, mahaifinsa ya sake tura shi karo ilimi a garin Bauchi, amma kuma neman ilimin bai yi tsawo ba saboda yana cikin karatun sai Allah ya bayyana sha’anin darikar Sheik Ibrahim Khaulahi, wato ‘’Faira’.
Daga nan ne ya shiga ciki, ya kuma zama daya daga cikin almajiran Sheikh Ibrahim Khaulak.
Malamin ya kuma kara da cewa; ”Saura kadan ya haddace Alkur’ani yana da shekara 13 amma sai suka shagala wajen noma da kiwo, don haka bai karasa haddacewa ba sai da ya kai shekara 19 zuwa 20.
Daga nan ya shiga karatu a wurin manyan malamai irinsu Malam Baba Sidi, da Malam Saleh, da Malam Baba Dan Inna Shaykh Tijani Usman Zangon Bare-bari da sheikh Abubakar Atiku Sanka Malam Shehu Mai Hula da Sheikh Abdulqadir Zariya.
A nan ne ya karɓi darikar Tijaniyya, tare da cikakkiyar ijazah kamar yadda mahaifinsa ya zama mukaddami.
Sheikh Dahiru ya zama fitaccen jagora a darikar Tijaniyya a Najeriya, a inda ya kasance mataimakin shugaban kwamitin fatawa na Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci na kasa– NSCIA.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi mutum ne babba a fannin ilimin addinin Musulunci, mutum mai ƙarfin imani, tawali’u da hikima.
Ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addinin Musulunci, koyar da Al-Kur’ani mai girma, tare da ƙoƙari wajen inganta ɗabi’a da ruhin bil’adama.
Ta hanyar makarantu da cibiyoyin ilmantarwarsa da dama, ya horar da dubban dalibai da suka haddace Al-Kur’ani kuma suka yada ilimin addini a sassan nahiyar Afrika.
Sheikh Dahiru Bauchi ya taba bayyana ce wa da gaske ne da farko yana da asiri da ake bawa yara suna haddar Alkurani da ya samu daga iyayensu da suka samu a Borno wajen Bare-Bari.
Amma daga bisani lokacin da Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana, ya ce ya roki Allah ya ba shi karamar haddar Alkur’ani, sai ya zama shi kenan an huta da nemo maganin karatun Alkur’ani.
Shehu ya riga ya roki Allah mutane su haddace Alkurani cikin sauki, inda yanzu yara masu shekaru biyar zuwa bakwai ke haddace kur’ani cikin sauki.
Malamin ya ce ya yi karatuttuka da dama amma wanda yake da shaida a kai shi ne haddar Alkur’ani, da tafsiri, wanda ya ce su kansu manyan malaman tafsirin sun tabbatar ya iya.
Gagarumin tasirin da marigayin ya yi a fannin tauhidi, fikihu, da tarihin Musulunci ya bar tabo mai ɗorewa a doron ilimi da da gina ruhin al’umma.
Ba wai malami ne kaɗai ba, a iya ce wa murya ce ta haɗin kai, zaman lafiya, yafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da kuma mabiya sauran addinai.
Sheik Dahiru Bauchi Malami ne na addinin Musulunci a Najeriya, mai riqo da tafarkin sufaye.
Shehu ne kuma muƙaddami ne a Ɗariƙar Tijjaniyya, yana Gabatar da tafsirin sa na Al’qur’ani da salon da shi kaɗai ya fara shi, wanda ake cema tafsirin Ƙur’ani a garin Kaduna a Babban Masallacin Juma’a na Tudun-Wada.
Wanda ɗansa yake ja masa baki, ya yin da shi kuma yake fassarawa ba tare da ya duba Littafi ba.
A 2009, an taba tsare shi a Saudiyya yayin aikin hajji, sakamakon rikicin fahimtar addini da ya kunno kai tsakanin kungiyoyin Darika, Izala da Shi’a.
Duk da haka, an sake shi, kuma ya ci gaba da jagorancinsa cikin nutsuwa.
Fitaccen malamin ya rasu yana da shekara 102 a duniya, ya bar ’ya’ya sama da 80.
Ya auri ’yar marigayi Sheikh Ibrahim Inyas, fitaccen malamin Tijaniyya na ƙarni na 20, inda ya bayyana cewa, baya ga kasancewa almajirin Sheik Ibrahim Inyass, akwai karin dangantaka mai karfi a tsakaninsu.
Ya ce, baya ga zama almajirin Sheik Ibrahim ya kuma zama khadiminsa, sannan ya zama surukinsa, don ya auri ‘ya’yansa har sau biyu, ya auri daya bayan ta rasu ya sake bashi auren daya.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu a ranar Alhamis 26 ga watan Nuwamba 2025 a garin Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya
Rasuwarsa ta bar babban gibi a ilimi, da karantarwa da jagoranci da kuma tarihin Musulunci a Najeriya.
Allah Ya jikansa da rahama Ya kyautata bayansa Ya kuma sa Aljannah Firdausi ce makomarsa.
