A rana mai kamar ta yau 1 ga watan Nuwambar shekarar 1925 ne, Kano ta kafa tarihi da saukar jirgin sama na farko a tarihin Najeriya.
Jirgin kirar De Havilland DH 9A ya sauka ne a filin wasan polo ta amfani da turbar dawakan da ake sukuwa da suka yi a matsayin hanya.
Mutukin jirgin, Sa, Authur Conningham ne mai mukamin Air Marshal a rudunar sojojin sama na turawan mulkin mallaka na Birtaniya, ya kuma tuko jirgin ne daga Helwan ta kasar Misra kafin ya iso Kano.
Connigham ya bayyana yadda ya tuko jirgin shi da abokan aikinsa biyu da yadda suka sauka da kuma irin tarbar da suka samu a cikin wani littafin rayuwarsa da marubuci Vincent Orange ya rubuta, kamar yadda Ja’afar Ja’afar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“A shekarun 1925 turawan kasashe Faransa da Beljiyum na shirye-shiryen fadada hanyar sardarwa zuwa kasashen Afrika da suke yiwa mulkin mallaka ta hanyar zirga-zirga ta jirgin sama.
“Kasar Birtaniya ta ga ba za a bar ta a baya ba, a watan Satumba Ma’aikatar Kula Da Sufurin Jirgin Sama ta sanar da cewa daya daga jiragenta guda uku kirar DH 9 A na rudunar sojin sama na 47, dake Helwan kusa Alqahira ta Masar zai tashi daga nan zuwa Kano.
“Za kuma su yi haka ne don gwaji da kuma kara gogewa a tafiya mai dogon zango musamman a kasashe masu yanayin zafi, musamma ma a inda ake da karancin kayyakin aiki na sauka da tashin jiragen sama.
“Kuma hakan zai ba ‘yan Najeriya su ga kwarewa da ingacin kimiyya da kuma fasahar jiragen Birtaniya”. In ji Connignham.
Jirgin ya tashi daga Helwan da karfe 7:00 na safe a ranar 7 ga watan Oktoba ya kuma sauka a Wadi Haifa mai kimanin 644 daga inda ya taso bayan kwashe kimanin awa takwas da minti ashirin a sama.
Jirgin ya tashi da misalin 4:50 na asubahi ranar, ya kuma sauka a Khartoum a kasar Sudan da yamma. Daga nan ya sauka a El Fasher a inda ya sha mai ya kuma yi facin tayarsa daya.
Tashin jirgin da laluben hanya ta amfani da alamun sawun ragumin alhazan dake tafiya aikin hajji, ta kai ga Abeche da kuma Fort Lamy a kasar Chadi, daga nan ya nufi Kano, a cewar matukin jirgin a littafin.
“Mun sauka a filin wasan dawaki na polo a Kano da misalin karfe 5 na yamma a rana ta shida da barin mu gida. Kafin mu zo, a inda muka tarar da cincirindon jama’a suna jiran isowarmu.
“Jama’ar da ta taru kallon jirgi kai 20,000. Jami’an tsaro kan dawakai na ta fama da su.” In ji shi.
Daga Kano, a cewarsa sai Conninghama da abokan aikinsa suka wuce zuwa Kaduna a ranar 6 da kuma Maiduguri kafin su koma gida Helwan a ranar 19 ga wata.
