
Ta tabbata cewa kasar Saudiyya ba ta karbar wata gawa daga wajen kasar domin binne wa haka kuma idan an mutu a cikinta ba a fita da gawar don binne wa a wani wuri.
Amma kasar ta yi wa iyalan Aminu Danatata da kuma musulmin Najeriya alfarmar cika wasiyyar attajirin na neman a binne shi a birnin Madina a wani lamari da ya kafa tarihi.
A ranar Talata 1 ga watan Yuli aka yi jana’izar attajirin dattijon bayan ya rasu a Abu Dhabi ta Hadaddiyar Daular Larabawa, an yi jana’izarsa a masallacin Manzon Allah tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi, aka kuma binne shi a makabartar Baqi’a mai daraja.

Tarihi ya nuna cewa mutane uku ne kadai kasar ta yi wannan alfarma a tarihi:
- Muhammad Al-Badr – Sarki na ƙarshe a ƙasar Yemen kafin juyin mulki ya kifar da mulkinsa. Ya rasu ne a birnin London a shekarar 1996.
- Zine El Abidine Ben Ali – Tsohon shugaban ƙasar Tunisia wanda ya yi mulki a ƙasar na tsawon lokaci kafin juyin juya hali. Ya rasu ne a birnin Jeddah, Saudiya, a shekarar 2019.
- Alhaji Aminu Alhassan Dantata – Fitaccen ɗan kasuwa daga Kano, Najeriya. Ya rasu ne a birnin Abu Dhabi, Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), ranar Asabar 28 ga Yuli, 2025.
Dukkan waɗannan fitattun mutane, iyalan su sun nemi izinin gwamnatin Saudiyya na yi musu sallar jana’iza a Masallacin Harami na Madina mai alfarma, buƙatar da ba kasafai ta kan amince da ita ba.

Domin wasu rahotannin bayan fage sun nuna cewa Sheikh Abubakar Mahmud Gummi da ya rasu ranar 9 ga watan Satumbar 1992 a wani asibiti a birnin Landan, iyalai da almajiransa sun nemi irin wannan alfarma, amma gwamnatin kasar ba ta bayar ba.
Marigayi Shehun malamin na daya daga cikin wadanda suka samu kyautar karramawa da kuma lambar yabo ta King Faisal a shekarar 1987, wadda kasar ke ba wa wasu fitattun mutane a duniya da suka hidimtawa addini.
Falalar binne mamaci a maƙabartar Baqi’a
Bagi’a maƙabarta ce da ke ɗauke da manyan sahababbai masu yawan gaske, domin kuwa bayanai na cewa an binne sahabbai fiye 10,000 a cikinta.
Wani malami a birnin Kano, Sheikh Abubakar Baban Gwale a hirarsu da BBC ya ce, maƙabartar na da falala mai girman gaske a Addinin Musulunci.
”Babba daga ciki shi ne kusanci da inda kabarin Annabi (S.A.W) yake tare da manyan sahabbansa guda biyu, Abubakar da Umar (R.A) da matansa da wasu ƴayansa.
Haka kuma ba a taɓa binne wanda ba musulmi ba a cikinta.
Sheikh Baban Gwale ya kuma ce an shar’anta wa duk wanda ya je aikin hajji, ya kuma je ”ziyara masallacin Annabi da kabarinsa to ana so ya je Baqi’a”.
Sannan Malamin Addinin ya ce, Manzon Allah ne ya fara jagorantar janaza a maƙabartar, da kuma ziyara, ”don haka duk wani hukunci da ya zo daga Annabi da ya shafi maƙabarta, to daga Baqi’a ya samo asali”.
”Duk abin da ka ji an faɗa dangane da annabi na abin da ya shafi maƙabarta to daga wannan maƙabarta aka samo hukuncin”, in ji malamin..

Ƴaƴan Annabi huɗu aka binne a Baqi’a
- Umm Kulthum
- Ruqayya
- Zaynab
- Ibrahim
Matan Annabi
Kusan duka matanSa Sallallahu alaihiwassalam a Baqi’a a aka binne su, in ban da Khadija bint Khuwaylid da aka binneta maƙabartar Mu’alla da ke Makka, Sai Maymuna bint al-Harith da aka binne a wata maƙabarta da ke arewacin Makka.
Sauran matan da ke kwance a Baqi’a sun ne:
- Aisha bint Abu Bakr as-Siddiq
- Sawda bint Zam’a
- Hafsa bint Umar ibn al-Khattab
- Zaynab bint Khuzayma
- Umm Salama bint Abi Umayya
- Juwayriyya bint al-Harith
- Umm Habiba, Ramla bint Abi Sufyan
- Safiyya bint Huyayy
- Zaynab bint Jahsh