Al’ummomi a jihohin da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa kan sabanin dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya da hada kai da Faransa wajen kawo wa Nijar cikas ta hanyar ba wa sojojin wurin don kafa sansanin soji da kuma daukar nauyin ‘yan ta’adda.
Gwamnatin Najeriya ta karyata zarge-zargen da kuma kiransu da marasa tushe ne ballantana na makama.
Sarkin garin Balle a Sokoto, Muhammad Illiyasu, ya ce bai taba ganin sojojin Faransa ko wasu dakaru a yankin ba, haka shima Muhammad Altine wani ɗan kasuwar shanu daga Jamhuriyar Nijar, ya musanta zargin sojojin Faransa a yankin, yana mai cewa zai sani idan akwai.
Talakawa dake zaune a garuruwan dake kan iyakar kasashen biyu sun na rokon a warware matsalar ba tare da shafar talakawa ba. Sun kuma roki a kasashen su warware matsalar cikin lumana.
La’akari da hakan zai janyo rufe iyaka wanda ke shafar raywuwarsu gaba daya
Wani dan kasuwa Hassan Tabani, daga Gada ya ce, rufe iyaka da aka yi a baya ya shafi kasuwanci sosai yana mai cewa zargin Tchiani mara tushe ne.
Haka suma mutanen jihohin Sokoto da Katsina da Borno sun bayyana illar rufe iyaka da aka yi a baya da cewa ya haddasa koma baya a tattalin arziki, tare da lalata kasuwancin tsakanin kasashen biyu.
Sun kuma yi kira ga gwamnoni biyu da su guji manufofin da za su haifar da husuma tsakanin yankunan kan iyaka.
Duk da zarge-zargen, mutane sun bayyana cewa ba su ga wata matsala a yanzu ba kuma suna ci gaba da zama lafiya.