Kakakin Majalisar Dokokin Kano, Jibril Ismail Falgore, ya taya gidan rediyon Premier Radio murnar cika shekaru huɗu da fara gabatar da shirye-shirye.
Kamaluddeen Sani Shawai, Kakakin shugaban ne ya sanar da hakan a watan sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
“Premier Radio a matsayin gidan rediyo mai jajircewa, mai hangen nesa da ƙudurin yada shirye-shiryen ƙasa da ƙasa.
“Nasarar da gidan rediyon ya samu cikin shekaru huɗu na nuna ƙarfin aiki tare, ƙwazo da jajircewa wajen isar da sahihan labarai da shirye-shiryen ilmantarwa ga al’ummar Kano da ƙasashen waje”. In ji shugaban.
Kakakin Majalisar ya kuma tabbatar da ƙudurin Majalisar dokokin ta jihar na yin aiki tare da gidan radion domin fahimtar da al’umma ayyukan majalisa da nauyin da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya dora mata.
