Al’ummar Jihar Neja sun koka cewa ƴan bindigar da aka yi sulhu da su a Birnin Gwari, Jihar Kaduna, na kutsawa garuruwansu suna aikata ta’asa sannan su koma inda suka fito.
A baya-bayan nan, gwamnatin Jihar Kaduna ta jagoranci sulhu da ƴan fashin daji a wasu yankunan da suka dade suna fama da hare-hare.
Dan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Rafi a Jihar Neja, Zubairu Isma’il Zanna, ya ce sulhun bai amfani jama’arsa, domin kafin hakan sun zauna lafiya, amma yanzu hare-haren sun tsananta.
A hirarsa da BBC, Zanna ya bayyana cewa ƴan bindigar da aka sulhunta a Kaduna sun addabi jama’arsa, inda a yanzu haka suke riƙe da mutane 132 da suka sace daga ƙauyukan Neja.
Matsalar ƴan fashin daji a Arewa maso Yamma na ci gaba da haifar da asarar rayuka da tagayyara al’umma, inda jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto da Neja ke fuskantar matsalar fiye da kowa.
