Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana dalilansa na nuna goyon baya ga ɓangaren Ministan Abuja Nyesom Wike a jam’iyyar PDP.
A hirarsa da BBC, Sule Lamido ya ce muddin ana son a samu sulhun da zai fitar da jam’iyyar daga rikici, dole masu ruwa da tsaki a jam’iyyar su rungumi kwamitin rikon jam’iyyar karkashin jagorancin Alhaji Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan ministan Abuja.
Ya ce hakan ya zama dole kasancewar ɓangaren ya samu amincewar hukumar zabe ta INEC, don haka shi ya kamata a bi a matsayin wani mataki na warware rikicin PDP da ya dabaibaiye jam’iyyar.
Wannan mataki na Sule Lamido ya zo da mamaki kasancewar yana cikin jiga-jigan PDP da suka yi adawa da Nyesom Wike wanda suke zargi shi ya jefa jam’iyyar cikin ruɗanin da take ciki inda har ta rasa gwamnoni da dama.
Sule Lamido ya yi adawa da babban taron PDP da ɓangaren Tanimu Turaki ya gudanar a birnin Ibadan inda ya nemi a rushe shugabannin riƙo da aka zaɓa bayan hana shi takara.
A watan Oktoba ne aka hana shi damar sayen fom ɗin tsayawa takarar shugabancin PDP, lamarin da ya sa ya garzaya kotu, kuma matakin da ya kai ga rusa sakamakon babban taron Ibadan.
Saidai Sule Lamido ya ce idan dai har mafita ake nema wa PDP don a yi takara a zaɓen da ke tafe dole duka ɓangarorin jam’iyyar a zo a zauna a yafi juna, sannan a kira Wike a zauna sulhu da shi. Ya kuma ce idan an shigar da kowane ɓangare a kwamitin riƙo na Wike, za a iya sake fasalta shi a gabatar wa hukumar zaɓe.
