Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi mazauna birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, da su kasance cikin shiri tare da gujewa wuraren cunkoson jama’a, bayan bayanan sirri sun nuna yiwuwar kai karin harin kunar bakin wake a cikin birnin.
Gargadin na zuwa ne bayan jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai a yammacin ranar Litinin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 108.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, jami’in hulda da jama’a na rundunar hadin gwiwar sojoji a yankin Arewa maso Gabas karkashin Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sanni Uba, ya ce hare-haren sun faru ne a wuraren da jama’a ke yawan taruwa a lokacin da ake shirin bude baki na azumin Ramadan.
Ya ce fashewar ta faru ne da misalin karfe 7:05 na yamma, lokacin da mutane da dama ke fita sayayya ko kuma suna kan hanyarsu ta komawa gida domin bude baki.
“Bayanai na farko sun nuna cewa ‘yan ta’addan na iya tura ‘yan kunar bakin wake da dama cikin Maiduguri domin kai hare-hare a wuraren da jama’a ke cunkoso, da nufin haddasa asarar rayuka da kuma tayar da hankalin jama’a,” in ji shi.
Jami’in ya bayyana harin a matsayin na rashin imani da tausayi, yana mai cewa ana zargin mayakan Boko Haram ne suka shirya kai hare-haren.
Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kara tsaurara sintiri, sa ido da kuma bincike kan bama-bamai a sassan birnin domin gano wadanda ake zargi da kuma hana sake faruwar wani harin.
A cewarsa, jami’an agajin gaggawa da suka hada da na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da kuma ma’aikatan lafiya sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Maiduguri da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda ake kula da su.
Rundunar sojin ta tabbatar wa mazauna birnin cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki domin tabbatar da tsaro, amma ta bukaci jama’a da su kasance cikin shiri.
“Mun bukaci mazauna Maiduguri su guji wuraren da jama’a ke cunkoso, su kuma rika sanar da jami’an tsaro idan sun ga wani motsi mai tayar da hankali ko kuma wani abu da aka bari ba tare da mai shi ba,” in ji sanarwar.
