Sojoji sun fatattaki Lukurawa daga Nijeria
Rundunar sojojin Nijeriya ta samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar Lukurawa daga kasar nan zuwa Jamhuriya Nijar
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin sanata Adamu Aliero, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.
Sanatan ya ce, samun nasarar fatattakar ‘yan bindigar ya tabbata ne a ranar Talata bayan da daukin da Ministan Tsaro tare da sauran masu ruwa da tsaki suka kawo wa jihohin da ‘yan ta’addan ke shirin yin kakagida.
“Mun fito karara mun fada wa ministan cewa idan aka yi sake da wadannan Lukurawan abin da ya faru ga yankin Arewa maso Gabas na rikicin Boko Haram, haka zai faru wannan yakin Arewa maso Yamma. Idan hakan ta faru ba zai haifar da da mai ido ba.
“La’akari da yadda yankin ke da yawan jama’a da arziki na kasar noma da kiwo da rafukan noman rani da kamun kifi da sauransu, don haka dole ne mu tsare yankin”. Inji shi
Ya kuma ce, sai dai duk da luguden wutar da sojin sama da kuma na kasa suka yi musu, ‘yan taddan sun makale a wasu kauyuka tare da takura musu har sai da sojon suka fatattake su tare da kora su zuwa Kasar Nijar.
Kain ficewarsu, ‘yan ta’addan sun kashe jama’ar da yawa da kuma sace dabbobi