
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a yayin da suke kokarin tayar da bama-bamai a wata gada da ke kan hanyar Dikwa zuwa Marte, a Jihar Borno.
A cewar rahoton, sojojin sun gwabza artabu da ‘yan ta’addan na tsawon lokaci kafin su kame su tare da kwato manyan bama-bamai guda biyu da aka tanada domin kai hari.
Wannan samame na cikin jerin hare-haren da dakarun Operation Hadin Kai ke kaiwa don kawar da ragowar ‘yan ta’adda daga yankin Arewa maso Gabas.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce cikin makon da ya gabata, dakarun sojin sun gudanar da gagarumin samame a yankunan Tafkin Chadi, Dajin Sambisa da Tsaunukan Mandara.
A cewarsa, samamen ya haifar da hallaka ‘yan ta’adda tara a kananan hukumomin Bama, Gwoza da Konduga na Jihar Borno.