Dakarun runduna ta 6 na sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyu tare da kwato muggan makamai a ƙaramar hukumar Takum dake Jihar Taraba.
A cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Kanar Aliyu Danja ya fitar a a ranar Talata ya ce, dakarun sun kai samame ne bayan samun bayanan sirri kan shirin kai hari a Chanchangi.
“Dakarunmu sun yi dauki ba dadi kan titin Demeva zuwa Chanchanji. An kuma kashe ɗan ta’adda guda ɗaya yayin da na biyun aka kashe shi a wani artabu a hanyar Demeva zuwa Gbudu. An kuma kwato bindiga da alburusai 16 da kuma babur guda ɗaya”. In ji shi.
Kwamandan rundunar Brigadier Janar Kingsley Uwa, ya jinjinawa dakarun bisa bajinta da ƙwarewar da suka nuna, tare da jaddada aniyar rundunar na ci gaba da fatattakar duk masu tada zaune tsaye a Taraba tare da dawo zaman lafiya a yankin.
