
Shugaban ‘yan bindiga, wanda Hedikwatar Tsaro ta Ayyana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, ya amince da yarjejeniyar sulhu a Jihar Katsina.
Isiya Kwashe Garwa yana cikin jerin manyan ’yan ta’adda 19 da ake nema ruwa a jallo a jihar.
Kwararre Kuma Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana haka a shafinsa na X a ranar Lahadi.Garwa, ɗan asalin kauyen Kamfanin Daudawa a Faskari, an dade ana danganta shi da kisan gilla da satar mutane da kuma kai hare-hare a dazukan Katsina da jihohin da Kuma makwabta.
Masanan tsaro sun taba bayyana shi a matsayin wani shugaban ‘yan bindiga da ke dagula zaman lafiya a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ta hanyar kai hare-haren ƙetare iyaka da kuma cin gajiyar rashin karfin hukumomi a yankuna.