
Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni mai shekara 80 da haihuwa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar NRM mai mulki.
Jam’iyyar ta ayyana Musevni a matsayin wanda zai yi mata takara a zaɓe mai zuwa.
A yanzu Musevni ya fi kowa jimawa kan mulkin ƙasar kasancewar ya shafe kusan shekara 40 yana mulkin ƙasar.
Musevni ya amince da takarar akuma jawabinsa na karba ya ce, idan ya yi nasara a zaɓen zai samu damar cimma muradinsa na mayar da ƙasar ”cikin jerin ƙasashen masu masu tasowa”.
Masu sukar shugaban, sun zarge shi da mulkin kama karya tun bayan da ya ƙwace mulkin ƙasar a matsayin jagoran ƴantawaye a 1986.
Tun daga lokacin ne ya riƙa lashe duka zaɓukan ƙasar da aka gudanar, yayin da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima har sau biyu, domin cire ka’idar shekaru da wa’adi domin ba shi damar ci gaba da zama a kan karagar mulki.