
Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya yi afuwa ga tsohon dan majalisar wakilai Farouk Lawan da kuma wasu karin mutane 175.
An dauki mataki afuwar ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da ta gudanar a ranar Alhamis a Abuja.
A sanarwar da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Bayanai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya ya ya sa hannun ta ce, Shugaba Tinubu yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misisi Anastasia Daniel Nwaobia da Lauya Hussaini Umar da Ayinla Sa’adu Alanamu, bayan an tabbatar da cewa sun nuna nadamarsu da shirin komawa cikin al’umma.

Sauran wadanda aka yi wa afuwar sun hada da tsohon ministan Abuja Mamman Vatsa, marubuci kuma tsohon jami’in sojan da aka kashe a shekarar 1986 bayan samunsa da laifin cin amanar ƙasa, bisa zarginsa da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin sojan Ibrahim Babangida. Ya samu afuwa ne yanzu bayan zartar masa hukuncin kisa shekaru arba’in da suka wuce.
Herbert Macaulay, ɗaya ne daga cikin fitattun ’yan gwagwarmayar samun ‘yancin kan Najeriya kuma wanda ya kafa jam’iyyar NCNC, ya samu afuwa kan hukuncin da hukumomin mulkin mallaka suka yanke masa a shekarar 1913.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya yi afuwa ga fursunoni 82, ya rage wa wasu 65 zaman gidan yari, sannan ya sauya hukuncin kisa na wasu mutum bakwai zuwa ɗaurin rai da rai.

Matakin yin afuwar ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Hakkin Yin Afuwa (PACPM) ya bayar, ƙarƙashin jagorancin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN).
Kwamitin ya duba bukatu 294, inda ya ba da shawarar yin afuwa ga fursunoni 82, afuwar kai tsaye ga mutum biyu, rage zaman gidan yari ga mutum 65, sauya hukuncin kisa ga mutum bakwai zuwa ɗaurin rai da rai, da kuma afuwa bayan mutuwa ga tsofaffin masu laifi 15.
Ka’idojin da kwamitin ya yi amfani da su sun haɗa da shekaru (60 zuwa sama), ciwon da ba ya warkewa, ƙuruciya (16 zuwa ƙasa), nuna kyakkyawan hali a gidan yari na tsawon lokaci, da nuna nadama, da sauransu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya ƙaddamar da kwamitin na PACPM a watan Janairu 2025 don inganta adalci, gyaran hali da kare haƙƙin ɗan adam a ƙasar.