
Shugaban Kamaru Paul Biya, mai shekaru 92 da haihuwa ya ce zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a ranar 12 ga watan Oktoba.
Idan ya tsaya takarar, zai zama karo na takwas da ya yi yana neman takarar zama shugaban kasar.
Paul Biya wanda shi ne shugaban ƙasa da ya fi tsufa ko yawan shekaru a duniya ya shafe shekaru fiye da 40 a karagar mulki.
Shugaba Biya ya ce, ya yanke shawarar tsayawa takara ne bayan kiraye-kirayen hakan da ake ta yi masa a ciki da wajen ƙasar.