
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, murnar nadin sarautar Sardaunan Zazzau.
Hakan na cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Bayanai Da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ne a ranar Juma’a.
Za a yi Bikin nadin ne a fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, a ranar Asabar, 11 ga Oktoba
“Sarautar Sardaunan Zazzau mukami ne mai girma da tarihi a Arewacin Najeriya, kuma wata alama ce ta yadda masarautar ke da cikakken kwarin gwiwa ga hikima, gaskiya da jajircewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa wajen cigaban al’umma”. In ji Tinubu a cikin sanarwar.
Shugaban Ƙasa ya kuma bayyana wannan karramawa a matsayin yabo ga kyakkyawan shugabanci da gudunmawar Sambo ga cigaban ƙasa.
Shugaban Ƙasa ya kuma jinjina wa Sarkin Zazzau bisa ci gaba da ɗora girma da mutunci ga waɗanda halayensu da shugabancinsu ke wakiltar manyan dabi’u, kishin ƙasa da mutuncin da masarautar ke girmamawa.
Yayinda Shugaba Tinubu ke yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa fatan alheri a sabon matsayin nasa na gargajiya, ya kuma bukace shi da ya ci gaba da zama abin koyi da jan ragamar matasa, tare da yin aiki kafada da kafada da shugabannin gargajiya da na al’umma don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.