Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tashi zuwa Birtaniya domin wata ziyara a hukumance bayan gayyatar da ya samu daga Sarki Charles na Uku da matarsa Sarauniya Camilla.
Shugaban ya tashi daga Abuja da safiyar yau Talata tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu.
Ana sa ran ziyarar, wadda ita ce irinta ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai zuwa Birtaniya cikin shekaru 37 karkashin bakuncin sarkin kasar a Windsor Castle, za ta kara karfafa alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
A yayin ziyarar, Sarki Charles III zai karbi bakuncin Shugaba Tinubu da uwargidansa a Windsor Castle daga ranar Laraba zuwa Alhamis.
Har ila yau, fadar za ta gabatar da wani baje koli na musamman na kayayyaki daga Royal Collection da ke da alaka da Najeriya.
Ana kuma sa ran Shugaba Tinubu da Sarki Charles za su yi ganawar sirri tare da haduwa da kungiyoyi da ke inganta tattaunawar addinai daban-daban a matakin kasa da kasa.
Ziyarar za ta kare da wata liyafar ta musamman (State Banquet) da za a yi domin karrama tawagar shugaban kasar .
A cikintsarin ziyarar, Shugaba Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a ofishinsa da ke 10 Downing Street, domin tattauna hanyoyin kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Ana sa ran ganawar za ta kai ga rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin fahimtar juna (MoU) da suka shafi kasuwanci, zuba jari, tsaro da kuma hadin gwiwar al’adu.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da za su gudana a ziyarar shi ne shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniyar samar da kudade da ta kai fam miliyan 746, tsakanin UK Export Finance da hukumomin Najeriya.
Ana sa ran kudaden za su taimaka wajen gyaran tashar jiragen ruwa ta Lagos (Apapa Quays) da kuma Tin Can Island domin inganta harkokin kasuwancin ruwa na Najeriya.
Haka kuma shugaban zai halarci wani baje koli na fasaha mai suna Nigerian Modernism, wanda zai nuna ayyukan fasahar zamani na Najeriya, tare da halartar wani taro da ’yan kasuwa na Najeriya da Birtaniya da kuma ’yan Najeriya mazauna kasashen waje.
Daga cikin manyan jami’an da ke cikin tawagar shugaban akwai shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, Ministan Albarkatun Kasa Dele Alake, Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, Ministar Al’adu Hannatu Musawa, Ministan Kudi Wale Edun, Ministan Sadarwa Bosun Tijani, Ministan Tsaro Janar Christopher Musa mai ritaya, da Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
