Ahmad Hamisu Gwale
Shirin AGILE mai tallafawa karatun ilimin mata, ya horar da Malaman makarantu hanyoyin da za su koyarda dalibai amfani da fasahar sadarwa da kuma amfani da naura mai Kwakwalwa Computer.
Taron bitar na kwana Uku na ci gaba da wakana a dakin karatu na Murtala Muhammad da ke Kano state Library, ana saran kammalawa ranar Alhamis 27 ga Fabrairu 2025.
Shirin na AGILE da ke karkashin maaikatar ilimi ta jihar Kano, na samun goyan baya daga bankin duniya da nufin tallafawa karatun ilimin mata.
Da yake jawabi a yayin taron shugaban shirin AGILE a Kano Mustapha Aminu ya bukaci malaman da su yi amfani da abin da suka koyawa domin koyar da daliban na su.
Haka zalika ya kuma ce wannan shiri na horar da daliban ba shi ne na farko ba, shirin na AGILE zai ci gaba da gudanar da wannan aiki.
Malaman makarantu daban-daban daga sassan birni da kauye ne suka halarci taron bitar da nufin amfani da abin da suka koya domin amfnar da dalibansu.
Ana saran karkare taron bitar a ranar Alhamis, 27 ga Fabrairu, wanda shirin ke zama damba ga shirin AGILE na ci gaba da bai wa bangaren ilimi muhimammanci.
