Fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu.
Sheihun Malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewar jikin malamin ya tashi a ranar Laraba, inda aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na ATBU.
Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin.
“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma.
“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.
Ana sa ran yin Jana’izar shehun Malamin a Bauchi
