
Mai magana da yawun marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da ministoci 22 da ya jagoranta, sun kammala zaman ta’aziyya a garin Daura, jihar Katsina.
Shehu ya ce, daga yau tawagar za ta koma Abuja, inda ake shirin gudanar da taron addu’a na musamman a fadar shugaban ƙasa domin marigayi Muhammadu Buhari.
Haka kuma za a ci gaba da karɓar gaisuwar ta’aziyya daga manyan jami’an gwamnati da sauran jama’a a babban birnin tarayya.
A cewar Garba Shehu, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, zai ci gaba da karɓar gaisuwar jama’a a gidan gwamnati da ke cikin birnin Katsina, yayin da uwargidan marigayin, Hajiya Aisha Buhari, tare da yaranta za su koma Kaduna gobe Juma’a domin ci gaba da karɓar gaisuwa a can.