
Majalisar Karamar Hukumar Dambatta ta bayyana damuwarta kan rashin biyan albashi ga Dagatai da masu unguwanni akalla 120, tsawon shekaru ashirin suna hidima ga al’umma.
Shugaban karamar hukumar Jamilu Abubakar ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da shugaban Kungiyar Ma’aikatar Kananan Hukumomi na jihar Kano NULGE, Comrade Ibrahim Muhd ya kai masa.
“Sakamakon wani binciken tantance ma’aikata da aka gudanar a baya, an gano cewa masu rike da mukaman Dagatai da masu unguwanni suna cikin mawuyacin hali na rashin samun albashi tsawon shekaru 20”. In ji shi.
Jamilu ya kuma ce, an mika koken ga gwamnatin jihar domin yin bincike kuma da zarar an kamala za a dauki matakin da ya dace.
A bangaren sa Comrade Ibrahim Muhd, ya ce ma’aikata a yankin na kokarin zuwa aiki kuma su na kokari wajen aiwatar da ayukansu yadda ya kamata, inda ya bukaci ma’aikatan karamar hukumar da su kasance masu halartar wuraren aikinsu akai-akai.