
Babban malamin ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya a ranar Alhamis
Marigayin shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Kasa na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS).
TRT ta rawaito cewa, za a gudanar jana’izarsa da misalin karfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.
.