
Fitaccen jarumin finafinan Hausa kuma shugaban Kungiyar Masu Shirya Finafinai Ta Kasa MOPPAN Alhaji Shehu Hassan Kano, ya jinjinawa gidan radio Premier tare da ba wa gidan kyautar Naira 30,000 don bukasa ayyukanta.
Shehu Hassan Kano ya bayar da kyautar ne a yayin bikin cika shekara biyu da kungiyar wasan kwaikwayo ta Mainagge Cultural Troupe dake gabatar da aikace-aikacenta a dandalin gabatar da wasanni a harabar gidan Radiyon dake unguwar Nassarawa a Kano .
Jarumin Finafinan na Kannywood, ya jinjinawa gidan radiyin da kuma mamallakinta Malam Abba Dabo a bisa namijin kokarin tallafawa kungiyar ta hanyar ba wa kugiyar dandalin wasan da har suka shekara biyu suna gabatar da al’amuransu.

“Hakika wannan ba karamin hobbasa bane kuma abin yabawa, kodayake duk wanda ya san Malam Abba Dabo ya san mai taimako ne, kuma mai sha’awar harkar raya al’adun gargajiya da ci gaban matasa ne.
Domin ni kai na yi rawar Koroso a karkashin kamfaninsa mai suna Arewa Communications a shekarar 1985 a Kaduna, a lokacin da babu wata kungiya da take da ‘yan rawar Koroso in ban da na Kano dake karkashin gwamnati.” In ji shi.
Cikin barkwansci ya kalli Malam Abba Dabo dale zaune a kujerar manayan baki ya ce.
” A madadina da kuma Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta MOPPAN ta Kasa, na ba gidan rediyon Premier Naira 20,000″.
Ya kuma juya ya kalli babban bakon mai masaukin baki, cikin nuna murnarsa, ya kuma kara da cewa, “Ganin yadda shugabanmu ya harde kafa, na kara Naira 10.000.”
Cikin dariya Shugaban ya kalle shi ya kuma nade hannua a kirji, ” to na nade hannu, sai a kara”.
Shehu Hassan ya zo ya durkusa a gabansa cikin ladabi yana gaisuwa cikin raha.
Taron na bikin cika shekarar Kungiyar ya samu halartar ‘yan wasan kwaikwayon dabe da na talbijin da tsaffin masu shirya finafinai na masana’antar Kannywood ciki har da Kabiru Nakwango da Shu’aibu Yawale da Malam Habibu Sani da suran matasan ‘yan wasan kwaikwayo da masu shiryawa.