Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnatin Kano ta nuna rashin jin dadinta kan fadan daba a Gwale, Dala, Nasarawa Fagge, da karamar hukumar Birni da kewaye.
Daraktan ayyuka na musamman na gidan gwamnati Ibrahim Umar, ne ya bayyana haka a Juma’ar nan yayin taron masu ruwa da tsaki kan fadan daba a jihar Kano.
Taron wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Kano ya samu halartar wakilan hukumomin tsaro, alkalai, malamai, shugabanin kananan hukumomi da masu sarautun gargajiya.
Daraktan ayyuka na musamman na gidan gwamnatin Ibrahim Umar, ya ce gwamnatin Abba Kabir Yisuf ba za ta zuba ido marasa kishi na tayar da hankalin al’umma ba.
Ya ce ce gwamnatin Kano na yin iya kokarinta wajen tabbatar da doka da oda da dawo da zaman lafiya cikin gaggawa a yankunan da abin ya shafa.
Ya kara da cewa hukumomin tsaro zasu cigaba da gudanar da ayyukan su a yankunan da rikicin dabar ya shafa har sai an samu tsaro.
Ibrahim Umar, ya ce gwamnatin jiha da kananan hukumomi zasu cigaba da yin aiki tare da musayar bayanai don hana faruwar irin wannan fadace fadace a nan gaba.
Ya ce manyan kalubalan dake haddasa wannan balahira sune kwaya da rashin aikin yi a don haka Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shirye-shiryen samun horo da hadin gwiwar hukumar samar da aikin yi ta kasa.
Ya ce gwamnati na cigaba da aikin gyara cibiyoyin koyon sana’o’i 26 da zarar an kammala zasu fara aiki.
Ya roki Sarakuna, Malamai, Jami’an tsaro da kungiyoyin fararen hula su hada kai wajen ilimantar da matasa kan illolin tashin hankali da miyagun kwayoyi.
Ya ce duk masu son tada hankali a Kano su sani cewa zasu fuskanci hukunci domin kuwa Gwamnati ba zata saurara musu ba.
Haka zalika Ibrahim Umar ya kuma ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ba za ta saurarawa masu yin katsalandan wajen yiwa bata garin hukunci ba.