Kasashe Somaliya da ta Habasha na shirin kwance damarar yaki bayan wani zama na sulshu a tsakaninsu da Kasar Turkiyya ta yi a Ankara.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne ya bayyana haka tare da ya jinjinawa shugaban Somaliya da kuma Firaministan Habasha a taron da taron da suke yin a sulhu a babban birnin na Turkiyya.
Ya kuma fadi halan ne saboda cimma matsaya a zaman sasantawar da suka yi mai wanda shugaban ya kira mai cike da tarihi da kuma gagarumar sadaukarwa.
Shugaban yayi wannan jawabi ne a yayin tattaunawar zaman lafiya da ya jagoranta a Ankara a ranar Talata.
“Na godewa shugaban Somaliya Hassan Shaikh Mahmud da Firaministan Habasha Abiy Ahmad, ta yadda bangarorin biyu suka amince da sanarwar hadin gwiwa domin warware takaddamar dake tsakaninsu.
“Babban fatan Ankara shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin Somaliya da Habasha, a wannan muhimmin yanki na Afirka.
“Turkiyya ta yi imanin cewa, yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashen Somaliya da Habasha suka amince da ita, za ta kafa tushe mai karfi na hadin gwiwa, da wadata, bisa mutunta juna. Inji shi.
Shugaban Somaliya Mohamud ya yaba da kokarin da Turkiyya ke yi na warware rikicin yankin iyaka da sabanin siyasa da aka dade ana yi tsakanin Somaliya da Habasha
Ya kuma ce kasarsa za ta ci gaba da kasancewa kawar Habasha ta gaskiya a ko da yaushe.
Ana sa ran tattaunawar za ta kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu game da ballewar yankin Somaliland.