
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da batan wani mahajjaci ɗanta a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da ibadar Hajjin 2025.
Mahajjacin, wanda aka bayyana sunansa da Sani Abubakar Danmaliki daga ƙaramar hukumar Kumbotso, ya bace ne a yayin gudanar da ayyukan Hajji a Saudiyya.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin da yake karɓar rahoton aikin Hajjin 2025 na jihar daga kwamitin kula da hajji.
A cewar Gwamna Abba, gwamnatin jihar tana aiki tare da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) domin gano inda mahajjacin ya ke.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wasu mahajjata biyu daga Kano da suka rasu a Saudiyya yayin aikin hajjin bana.