
Hukumomin Saudiya sun dage Jana’izar marigayi Aminu Dantata zuwa gobe Talata.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Yada Labarai na Kasar nan Mohammed Idris a hirarsa da BBC a ranar Litinin a kasar Saudiyya.
Tawagar ta kunshi Ministan Shari’a Yarima Lateef Fagbemi SAN da Karamin Ministan Samar Da Gidaje Abdullahi Yusuf Atta da Minista Yada Labarai Mohammed Idris da Dakta Bashir Aliyu Umar da Sheikh Aminu Daurawa da kuma Khalifa Abdullahi Mohammed Limamin Masallacin Dantata a Abuja.
Tawagar Gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi da tuni ta isa Saudiyya tun safiyar Litinin
Ayarin gwamnati tarayya da a jiha sun hadu da ma’aikatan Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya karkashin Ambasasa Mu’azzam Ibrahim Nayay wanda suka yi ta kai-komo don ganin kasar ta amince da bukatara marigayin.