
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira da a gyara tsarin shari’a na Najeriya, yana mai nuna damuwa kan yadda talakawa ke fuskantar rashin adalci, yayin da masu kuɗi ke kaucewa hukunci.
Ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta kasa (NBA) da aka gudanar a Enugu, inda ya ce rashawa da rashin daidaito suna lalata sahihancin tsarin shari’a.
Sultan ya yabawa NBA bisa taken taron na bana, yana mai cewa lauyoyi su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da mulkin doka da adalci.
Sultan Sa’ad ya jaddada cewa masana shari’a dole ne su ci gaba da zama masu jajircewa wajen tabbatar da mulkin doka, adalci, da daidaito.
Ya ce rashin adalci na haifar da rashin yarda da tsarin doka, wanda ke iya janyo tashin hankali da daukar doka a hannu.