
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a kasar nan.
Obasanjo ya bayana hakana ne a cikin wani sabon littafin da ya wallafa mai suna “Najeriya a Jiya da kuma gobe” da turanci
Tsohon shugaban ya fitar da littafan biyu ne don murnarsa cika shekaru 88 da haihuwa a ‘yan kwanakin nan.
A rawaito cewa a shafi na 14 na littafin, Tsohon shugaban ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya.
Tsohon shugaban ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya.
“Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.
“Don haka dole ne a dawo da mutunci da kuma ƙimar sarautar gargajiya domin tana taka rawar gani a ci gaban ƙasa.” In ji shi
Obasanjo ya kuma gargaɗi shugabanni cewa idan ba su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta ba, hakan na iya haifar da rikici a nan gaba.