
Sanatar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan – da aka dakatar – ta yi kira ga babban sifeton ƴansandan ƙasar, ya mayar mata da jami’an tsaronta da aka janye mata lokacin da majalisa ta dakatar da ita.
Kiran na zuwa ne bayan da wasu mahara suka auka wa gidan kakanninta da ke jihar Kogi ranar Talatar da ta gabata.
Sanata Natasha ta yi zargin cewa ita aka ƙudiri aniyar kai wa harin, tana mai cewa maharan sun kai harin ne saboda a tunaninsu tana gidan.
Harin ya lalata wasu ɓangarorin gidan, wanda ƴar majalisar ta ce na kakanta ne.
To sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin, kamar yadda ta yi ƙarin haske.
A watan da ya gabata ne dai Majalisar Dattawan Najeriyar ta dakatar da ƴar majalisar tsawon wata shida, tare da tsayar da alawus-alawus da ake ba ta da jami’an tsaron da ke ba ta kariya, saboda zargin rashin ɗa’a.
Dakatarwar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata Godswill Akpabio da yunƙurin cin zarafi na lalata da amfani da ofishinsa wajen tursasawa da kuma daƙile mata aikinta.